Tuesday 9 December 2025 - 22:09
Abubuwan Dubawa Goma Sha Biyu (12) Na Ayyukan Alkur'ani A Makarantun Ilimin Addinin Musulunci (Hauza)

Hauza/Shugaban Makarantun Ilimin Addinin Musulunci (Hauza) Ayatullah Alireza A'arafi, a taron masu fassara da kuma tafsirin Alkur'ani mai girma ya bayyana cewa, Alkur'ani shi ne kawai rubutu na asali wanda ya fito daga sama, kuma bukatar gama-gari ne ga dukan bil'adama. Ya ce:"Duk da nasarori da yawa da aka samu a fagen tafsiri da ilimin Alkur'ani, makarantun ilimin addinin Musulunci har yanzu suna fuskantar tafiya mai nisa kafin su isa ga girman Alkur'ani da bukatun duniya. Dole ne su shiga fagen da manufa ta wayewar kai, bincike mai zurfi, da kuma fuskantar duniya.

A cewar rahoton wakilin Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah A'arafi a taron malaman tafsiri da masana Alkur'ani, wanda aka gudanar a ofishinsa, ya taya murna da ranar haihuwar Sayyida Fatima Zahra (AS) da kuma ranar haihuwar Imam Khomeini (RA), ya kuma jaddada wajibcin girmama waɗannan manyan ranaku da mutunta matsayin uwargidan duniya da lahira.


Girmama Matsayin Sayyida Zahra (SA) Da Hukunta Dabi'o'in Jahilai

Shugaban Makarantun Ilimin Addinin Musulunci ya yi magana game da wasu kalamai da ba su dace ba da ake yi game da ɗaukakar martabar Sayyida Fatima Zahra (AS). Ya bayyana cewa: "Duk wasu maganganun jahilci da ta keta darajar wannan babbar mai martaba, idan ta fito ne daga wadanda ba su da ilimi, abin takaici ne kuma abin bakin ciki. Dukkanmu muna da hakki mu kare Uwar Jikokin Annabi, mai-ɗauke da albarka mara-iyaka ta Allah, ta hanyar da ta dace da ilmi, hikima da kuma jarumtaka."

Imam Khomeini (RA); Rana Da Ta Haskaka Tunanin Musulunci

Memba a cikin Babbar Majalisar Makarantun Ilimin Addinin Musulunci, yayin girmama tunanin da kuma tafarkin Imam Khomeini (RA), ya ce: "Girman Jagoran Mu (Imam Khomeini) kamar rana ce mai haske wadda shekaru ɗaruruwa ba za a iya samun irinta cikin sauƙi ba. Shi ne ya ɗaga tutar Musulunci a duniya, kuma ya haifar da babban sauyi a rayuwar addini da wayewar kai. Ranar haihuwar Imam (RA), tunawa ce da haihuwar wanda ya kafa wannan babban motsi, mai kawo sauyi da kuma gina wayewar kai."
Girmama Shuhada da Jaddada Jarin Asali Na Juyin Juya Halin Musulunci

Ayatullah A'arafi, lokacin da yake nuni ga matsayi mai girma na shuhada, ya kara da cewa: "Dole ne mu tuna da manyan shuhada, shuhadan tsaron kasa mai tsarki, shuhadan shekaru biyu da suka wuce, da fiye da shuhada dubu biyar daga cikin makarantun ilimi da malaman addinin Musulunci. Tsarin shahada a cikin makarantun ilimi, tsari ne mai haske kuma babban kashin bayanmu. Imam Khomeini (RA) da shuhada su ne jarin da ya gina juyin juya hali na musulunci."

Shugaban makarantun ilimin addinin musulunci ya yaba wa jagoran juyin juya halin Musulunci saboda tallafi da shiryarwa akai-akai ga makarantun ilimi, sannan ya yaba wa manyan Maraji'an takalidi na addinin musulunci a matsayin manyan jagororin makarantun ilimi.

Rahoto game da Halin da Sabbin Ci gaban Ayyukan Alkur'ani a Makarantun Hauza

Ayatullah A'arafi, yayin godewa malamai da masu tafsiri, ya ce: "A cikin ayarin Alkur'ani na makarantun Hauza, muna ganin sabbin ci gaba masu matukar kima; tun daga matasa masu hazaka har zuwa manyan malamai da suka gabatar da sabbin shirye-shirye da kirkire-kirkire a fagen Alkur'ani."

Shugaban makarantun ilimin addinin musulunci, da yake bayar da rahoton sauye-sauyen da aka samu a fagen Alkur'ani bayan juyin juya halin musulunci, ya nuna fagage hudu:

1. Daruruwan cibiyoyin ilimi da bincike na Alkur'ani a manyan matakai suna aiki.
2. An samar gomomin mujallu na musamman, dubban kasidu, da ɗaruruwan binciken kammala karatun digiri (projects).
3. An samar da gomomin software na Alkur'ani, haka kuma an tsara gomomin cikakkun tafsiri na tsari da na jigo.
4. Fassarorin Alkur'ani da tafsirai sun yadu zuwa harsuna a duniya.

Shugaban makarantun Hauza ya bayyana cewa: "Irin wannan ayyuka babu su kafin juyin juya halin musulunci, kuma an same su ne saboda albarkar juyin juya halin Musulunci da jajircewar malamai da ɗalibai."


Alkur'ani; Saukakken Rubutun Asali Daga Sama kadai a Duniya

Mamba a cikin Babbar Majalisar Makarantun Ilimin Addinin Musulunci, yana mai nuni ga binciken tarihi game da saukakkun littattafai, ya lurar: "A duk faɗin duniya, babu wani rubutu da ke da'awar cewa ya zo daga sama ba tare da gurbatawa ba kuma ba tare da canji ba. Alkur'ani shi ne kawai rubutun Allah na asali kuma mara kura, kuma muna da hujjoji bayyanannu ga wannan gaskiya."

Ayatullah A'arafi ya yi imani cewa: "Alkur'ani littafi ne na halitta kuma na shari'a; a cikin Nahjul Balagha akwai fiye da sifofi hamsin masu haske game da girman Alkur'ani, waɗanda kowannensu yana buƙatar tattaunawa ta musamman."

Bukatar Duban Duniya a Ayyukan Alkur'ani

Shugaban makarantun ilimin addinin Musulunci ya bayyana cewa: "Duk da dukkan ayyuka, a gaban girman Alkur'ani da kuma gaban buƙatar duniya daga mutane biliyan bakwai na yau har zuwa biliyoyin mutane na gaba, aikinmu dan kadan ne. Masu sauraron makarantun ilimi ba Iran da duniyar musulunci ba ne kadai; dukkan bil'adama ne masu sauraronmu."
Tsare-tsare Da Aka Shawarta Don Inganta Ayyukan Alkur'ani:

Ayatullah A'arafi a ci gaba da gabatar da jerin tsare-tsare na dabaru don ayyukan Alkur'ani na makarantun ilimi a nan gaba ya bayyana:

1. Bukatar Duban Wayewar Kai Ga Alkur'ani: Alkur'ani rubutu ne na wayewar kai kuma yana shimfiɗa inuwa a kan kowane fanni na rayuwar ɗan adam. Duba na wayewar kai ya kamata ya shiga cikin kowane fanni na Alkur'ani da kuma cikin tsarin kowane fanni na makarantun ilimi. Fahimta ta ragewa ko wuce gona da iri game da wayewar kai na addini ba daidai ba ne; Alkur'ani yana ba da hanya mai daidaito, mai ma'ana, kuma mai shiryarwa.
2. Ƙarin Bayyanar Alkur'ani a Duk Ilimin Musulunci: Alkur'ani ya kamata ya shiga cikin fikihu, Usul, falsafa, aƙa'id, hadisi da sauran ilimin Musulunci sosai. A yanzu ma akwai; amma ya kamata ya fi haka yawa.
3. Ƙarfafa Hanyar Bincike a Tafsiri: An gabatar da sabon ka'idoji a makarantun ilimi, wanda ya samar da hanya ta hukuma don gudanar da "darussan bincike a cikin tafsiri". Manyan littattafan tafsiri kamar Majma' al-Bayan da Al-Mizan za a shigar da su cikin shirin koyarwa a hukumance.
4. Ci gaban Tafsiri Zuwa Ilimin Yan Adam da Sababbin Batutuwa: Ya kamata a haɓaka fannonin ilimin ɗan adam masu alaƙa da Alkur'ani. Manyan matakan makarantun ilimi ya kamata su taka rawa mai mahimmanci a wannan fagen.
5. Tsara Tsarin Rubutattun Darussa da Faɗaɗa Darussan Tafsiri: Ya kamata a ci gaba da tsarin rubutawa da rikodin darussan tafsiri da rubuce-rubuce da ilimi.
6. Ƙarfafa Tafsirin Ruwaya: Makarantun ilimi suna buƙatar ayyuka masu zurfi, faɗi, da tsari a wannan sashe.
7. Mai Da Hankali Musamman Ga Fagen Duniya da Fassarar Ma'anoni Na Alkur'ani: Mai tafsiri da mai bincike ya kamata ya san abin da duniya ke faɗa game da Alkur'ani da kuma abin da masu sauraron duniya ke buƙata. Sabbin fassarori da ayyuka masu hikima wajen isar da ma'anoni sun zama dole.
8. Amfani mai Fadi Da 'Artificial Intelligence 'AI' a Nazarin Alkur'ani: 'AI' yana canza ma'auni na nan gaba. Idan muka gafala muka rasa shi, za mu kasance a baya. An fara ayyuka masu kyau a Cibiyar Nur kuma ya kamata a ƙarfafa su sosai.
9. Ƙirƙirar Taswira Cikakke Na Alkur'ani da Rarraba Ayyuka Na Ƙasa: Ya kamata a daidaita tarin cibiyoyin Alkur'ani cikin tsari cikakke. Ci gaba da musayar ra'ayi tsakanin malamai da cibiyoyin tafsiri ya zama dole.
10. Tafsiri, Wa'azi da Alaka Mai Tasiri Da Matasan Zamani: Samar da tsari da shirye-shiryen Alkur'ani da suka dace da tsatson zamani ɗaya ne daga cikin mahimman ayyukan makarantun ilimi.
11. Nazarin Batutuwan Alkur'ani da Tsara Tsari Na Bincike: Ya kamata a cika, sake ginawa, kuma a ba da tarin batutuwan Alkur'ani ga binciken kammala manyan makarantun karatun digiri.
12. Horar da Manyan Masana Tafsiri Lamba Daya: Bayan horar da ƙwararrun ma'aikata a matakai daban-daban, makarantun ilimi ya kamata su haɓaka manyan malaman kimiyya a fagen tafsiri don biyan bukatun nan gaba.


Jaddada Ci Gaba da Taron Ƙwararru da Karɓar Ra'ayoyin Malamai


Ayatullah A'arafi a ƙarshe, yayin da yake jaddada ci gaba da tarurrukan ƙwararru da karɓar ra'ayoyin malamai, ya ce: "Dole ne dukkanmu mu yarda cewa a gaban Alkur'ani, muna da gazawa da gafala da yawa, amma tare da himmar hada kai da hangen nesa na wayewar kai, zamu iya ɗaukar muhimman matakai a cikin bayyana ilimin Alkur'ani da isar da saƙon Allah zuwa ko'ina cikin duniya."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha